Shahararren mawaƙin hip-hop, Naira Marley, ya bukaci a daina danganta kuskuren da yake yi da addinin Musulunci, yana mai jaddada cewa addinin nasa kamalalle ne kuma rahama.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, mawaƙin ya bayyana cewa duk wani abu mai kyau da yake aikatawa daga koyarwar addininsa ne, amma kuskuren da yake yi ajizancinsa ne a matsayin ɗan Adam.
“A daina danganta kuskuren da nake yi da addinin Musulunci… Shi addinin Musulunci rahama ne kuma shine addinin Allah kuma kamalalle ne. Amma ni, a matsayina na Musulmi, ɗan Adam ne ajizi, ina kuskure. Don haka, kuskure nawa ne ba na addinina ba,” in ji shi.
Wannan furuci na Naira Marley ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta, inda mutane ke tofa albarkacin bakinsu kan batun. Me kuke tunani?