API

Mali, Burkina Faso da Nijar Sun Kakaba Haraji kan Kayayyakin Shigowa daga Najeriya da ECOWAS

 Kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar sun sanar da kakaba sabon harajin kashi 0.5 cikin 100 kan dukkan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje, ciki har da Najeriya da sauran mambobin kungiyar ECOWAS. Wannan mataki na zuwa ne bayan ficewar wadannan kasashe daga ECOWAS, tare da kokarin samar da kudaden tafiyar da sabuwar kawancensu ta kasashen Sahel (AES).



A cewar sanarwar da aka fitar, an amince da wannan haraji ne a ranar Juma’a, 28 ga Maris, 2025, kuma ya fara aiki nan take. Harajin zai shafi dukkan kayayyakin da ake shigowa da su, banda tallafin jin kai.


Wannan mataki yana nuni da karshen cinikayyar ’yanci da aka saba yi a tsakanin kasashen yammacin Afirka, wanda ke kara bayyana rabuwar kai tsakanin kasashen uku da sauran mambobin ECOWAS.


A baya, ECOWAS ta kakaba takunkumi kan wadannan kasashe domin tilasta musu komawa mulkin farar hula, amma hakan bai yi tasiri ba.


Kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar na fuskantar kalubalen tsaro na ’yan bindiga masu alaka da al-Qaeda da ISIS, wanda ya kashe dubban mutane tare da tilasta miliyoyi yin hijira.