Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Najeriya (EFCC) ta kaddamar da bincike mai zurfi kan zargin damfarar Naira tiriliyan 1.3 da ake dangantawa da wani tsarin saka hannun jari na intanet da kamfanin CryptoBank Exchange (CBEX) ke gudanarwa.
EFCC ta bayyana cewa tana aiki kafa-da-kafa da Interpol, hukumar ‘yan sanda ta duniya, domin bankado duk masu hannu da shuni a wannan badakala, ciki har da wadanda ke cikin gida da kuma kasashen waje.
Rahotanni sun nuna cewa CBEX wani kamfani ne da ake zargin ana gudanar da shi ne ta hadin gwiwar wasu ‘yan kasashen waje da kuma ‘yan Najeriya, wanda ya ruguje a ranar Litinin da ta gabata. Wannan rugujewar ta jefa dubban masu zuba jari cikin halin kunci bayan asusun su na kamfanin ya toshe.
Wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun wayi gari asusun su babu ko sisi, yayin da kamfanin ke bukatar karin kudi daga hannun jari kafin a bude musu damar cire kudadensu – wani abu da ya kara tayar da hankali.
Kodayake hukumomi ba su fitar da takamaiman adadin asarar ba tukuna, rahotanni daga majiyoyi daban-daban sun yi hasashen cewa an yi asarar da ta kai kimanin dala miliyan 847, kwatankwacin Naira tiriliyan 1.3, abin da ya shafi masu zuba jari daga ciki da wajen Najeriya.
Kamfanin CBEX ya janyo hankalin jama'a ne da alkawarin ribar kashi 100 cikin 100 a cikin kwanaki 30 ta hanyar kasuwancin intanet. Amma tun daga ranar 9 ga watan Afrilu, 2025, kamfanin ya fara nuna alamun durkushewa.
Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya ce tun kafin kamfanin ya durkushe, hukumar ta samu bayanan sirri kuma ta riga ta fara bincike.
“Mun fara bincike tun kafin rugujewar. Yanzu da lamarin ya tabbata, za mu zakulo duk wanda ke da hannu a ciki,” in ji shi yayin zantawa da manema labarai a ranar Talata.
Oyewale ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa EFCC na aiki tukuru wajen wargaza duk wani shirin damfara makamancin CBEX.
“Akwai shafukan damfara irinsu CBEX a sassa daban-daban na ƙasar nan. Muna ci gaba da bankado su, tare da hadin gwiwa da hukumomin cikin gida da kuma Interpol domin kama masu aikata wannan laifi a duk inda suke,” in ji shi.