API

Yadda Atiku, El-Rufai, Tambuwal da Pantami Suka Gana Da Buhari A Kaduna

A wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, an ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma dan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, yana ziyarar gaisuwar Sallah ga tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a gidansa da ke Daura, jihar Katsina.



Atiku Abubakar ya bayyana wannan ziyara a shafinsa na sada zumunta a matsayin wata ziyara ta musamman domin nuna girmamawa, gaisuwa da haɗin kai a irin wannan lokaci na bukukuwan Sallah, musamman da kasancewarsa Waziri na Adamawa wanda ke da alhakin wakiltar Lamidon Fombina a lokutan da suka dace.


Buhari, Atiku, El-rufai, Pantami da sauran tawaga yayin Sallar Juma'a a Kaduna
Buhari, Atiku, El-rufai, Pantami da sauran tawaga yayin Sallar Juma'a a Kaduna

A cikin faifan bidiyon, an hangi manyan jiga-jigan siyasa da suka hadu da Atiku a wajen ziyarar, ciki har da tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai, tsohon ministan sadarwa Isa Ali Pantami, tsohon ministan shari'a Abubakar Malami (SAN), da tsohon gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, tare da wasu fitattun 'yan siyasa.


Sai dai ziyarar ta janyo cece-kuce daga masu fashin baki kan al'amuran siyasa. Wasu na ganin hakan wani yunkuri ne daga Atiku domin sake gina dangantaka da manyan jiga-jigan siyasar Najeriya tare da shirya tsaf don fuskantar babban zaben 2027, inda ake hasashen zai kara fafatawa da shugaba mai ci, Bola Ahmed Tinubu.

A daya bangaren kuma, wasu na kallon ziyarar a matsayin ta al’ada ce kawai ta nuna girmamawa da mutunta tsohon shugaban kasa a lokacin Sallah, ba tare da wata manufa ta siyasa kai tsaye ba.



Duk da haka, wannan ziyarar ta sake jaddada cewa Atiku Abubakar na ci gaba da taka rawa a sahun gaba na siyasar Najeriya, yana gina ƙawance da masu faɗa a ji a fadin ƙasa, musamman a irin wannan lokaci da ya zama na shiri da tunani kan makomar shugabanci bayan 2027.