API

Anyi Sulhu Da Sasanci Rigamar Tsakanin Najeriya Da Nijar

An kammala wani muhimmin taro na diflomasiyya tsakanin kasashen Najeriya da Nijar, wanda ya gudana a birnin Yamai, babban birnin kasar Nijar. A wannan zama, Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ne ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa Nijar, inda aka karɓe su da karamci daga Ministan Harkokin Wajen Nijar, Bakari Ya’u Sangaré.



🕊️ Me Taron Ya Kunsa?

A yayin ganawar, an cimma yarjejeniya tsakanin kasashen biyu domin:

  • Kara fahimtar juna da karfafa zumunci,
  • Tabbatar da zaman lafiya a iyakokin kasashen,
  • Inganta huldar tattalin arziki da cinikayya,
  • Da kuma yaki da miyagun laifuka da ke kan iyaka, musamman fasa kwauri da ta'addanci.


Tabbacin Gamsuwa Daga Bangarorin Duka

Daga karshe, kowanne bangare ya bayyana jin dadinsa da gamsuwa da yadda aka gudanar da taron. Ministan Nijar, Bakari Ya’u Sangaré, ya bayyana cewa:

"Lallai mun yi nasarar jan aiki. Wannan ganawa ta nuna cikakken hadin kai da nufin tabbatar da zaman lafiya a yankin."

Haka zalika, Ambasada Yusuf Tuggar ya yaba da karɓar da aka yi musu tare da jaddada aniyar Najeriya na ci gaba da aiki tare da Nijar wajen samar da ci gaba da kwanciyar hankali a yankin yammacin Afirka.