API

Tinubu Ya Ba da Umarnin Kama Wadanda Suka Kashe ’Yan Arewa a Edo

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah-wadai da kisan gillar da wasu ’yan bangar siyasa suka yi wa wasu matafiya a Jihar Edo yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Arewa.



Shugaba Tinubu, wanda ya bayyana damuwarsa kan wannan mummunan al’amari da ya faru a ranar Alhamis, ya umarci rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da cikakken bincike tare da hukunta wadanda suka aikata wannan ta’asa.


Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci cin zarafin ’yan kasa ko zubar da jinin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.


Shugaban kasar ya jaddada rashin amincewarsa da daukar doka a hannu, yana mai nanata cewa kowanne dan Najeriya na da ’yancin yin zirga-zirga cikin lumana a dukkan sassan kasar ba tare da tsangwama ba.


Bugu da kari, Tinubu ya jinjinawa Gwamnan Jihar Edo, Sanata Mondaya Okpebholo, da sauran shugabannin al’ummar yankin Uromi kan yadda suka gaggauta daukar matakan da suka hana rikicin tsananta.