Sarkin Musulmi ya kuma bukaci Gwamnati ta sauki matakin gaggawa.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya yi Allah waddai da kisan wasu ’yan Arewa da aka yi a Jihar Edo, yana mai kira ga gwamnati da ta dauki matakin gaggawa domin hana sake afkuwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba.
“Muna Allah waddai da wannan abu da ya faru a Jihar Edo. Abin takaici ne, kuma ya kamata gwamnati ta dauki matakin gaggawa domin hana irin wannan kisa,” in ji Sarkin Musulmi.
Ya bukaci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin gano wadanda suka aikata wannan ta’asa tare da tabbatar da adalci ga wadanda suka rasa rayukansu da iyalansu.
Har ila yau, Sarkin Musulmi ya jaddada bukatar karfafa zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’ummar Najeriya, yana mai cewa Najeriya kasa daya ce, don haka dole ne a tabbatar da adalci ga kowa ba tare da nuna bambanci ba.
Sarkin Musulmi ya kuma yi kira ga shugabanni da su dauki nauyin kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa, domin hana yaduwar tashin hankali da dakile daukar doka a hannu.