Jagoran Darikar Kwankwasiyya ta Duniya, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana alhininsa kan kisan gilla da aka yi wa matafiya 16 daga Arewacin Najeriya a yankin Udune Efandion na Uromi, Jihar Edo.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya ce:
“Ina matukar damuwa da mummunan abin da ya faru na zalunci mai cike da keta doka a kan matafiya daga Arewacin Najeriya a Jihar Edo. Wannan bala’i, wanda ya auku a ranar 27 ga Maris, 2025, wani abin takaici ne da ke kara tunatar da mu muguntar daukar doka a hannu.”
Ya jaddada cewa kowane dan kasa yana da ’yancin yin tafiye-tafiye cikin lumana ba tare da wata tsangwama ko barazana ba.
Saboda haka, Kwankwaso ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike domin gano wadanda suka aikata wannan ta’asa tare da tabbatar da cewa an hukunta su bisa doka.
A karshe, ya roki Allah Ya jikan wadanda suka rasu tare da mika ta’aziyyarsa ga iyalansu da dukkan al’ummar da abin ya shafa.