API

Kiris Ya Rage Na Hakura da Takara A Zaben 2023 - Inji Shugaba Tinubu

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Matsalolin da Ya Fuskanta a Hanyar Samun Nasara

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana irin ƙalubalen da ya fuskanta a tafiyar sa ta neman shugabancin ƙasar, yana mai cewa da ikon Allah ne kawai ya samu nasarar da ke gabansa a yau.

A cikin jawabin da ya gabatar a wurin taron godiya, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa akwai lokutan da matsaloli suka yi masa yawa har ya kusan janye daga takara.




"Ban da Kuɗi, Ban da Taimako, Amma Na Ci Gaba"

Shugaban ya bada misali da wani lokaci da ɗaya daga cikin masu kusa da shi ya zo gidansa da misalin ƙarfe 3:30 na dare yana bukatar naira 50,000 domin kaiwa wa wani dan'uwansa abinci saboda rashin kuɗi da matsin tattalin arziki a wancan lokaci.

"Ina zaune a ɗaki da misalin ƙarfe 3:30 na dare sai wani daga cikin mutanena ya zo ya ce yana buƙatar naira 50,000 domin kaiwa wa wani ɗan’uwansa abinci, saboda babu kuɗi kuma babu abinci. Amma kuɗi sun kare a bankuna, mutane na hayewa kan kaunter don samun kuɗi," in ji Shugaban.

A cewar Tinubu, mutumin da ya zo da bukatar ya tambaye shi cewa, "Mene ne kake nema?" Sai ya amsa da cewa, "Ina takarar shugaban ƙasa."

Amma mutumin ya mayar da martani da cewa, "Ba don kanka ba? Ba don danginka ba?" Sai Tinubu ya ce, "A'a, don shugabancin ƙasa."

Mutumin ya sake tambaya, "To ka bani naira 50,000." Tinubu ya ce ya ba shi, amma kafin mutumin ya fita daga gidan, sai ya ce, "Ni dai bana ganin za ka yi nasara."

Tinubu ya bayyana cewa ya yi murmushi sannan ya ce masa, "Tabbas zan yi nasara. Idan na yi kuma ka dawo neman aiki, ba zan ba ka ba."

Kusan Na Hakura da Takara - Tinubu

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa bayan wasu awanni, sai wani daga cikin danginsa ya kira shi yana nuna godiya bisa gudunmuwar da aka ba su.

Ya ce a wancan lokaci har ya kusan janyewa daga takarar, amma wata ƙungiya ta ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ta ƙarfafa masa gwiwa tare da ba shi goyon baya.

"Masari ya ce min kada in juya baya, muna tare da kai," in ji Shugaban.

A ƙarshe, Tinubu ya bayyana godiyarsa ga duk wanda suka mara masa baya, yana mai cewa irin azama da sadaukarwa da ya gani daga masu kaunarsa ne suka sa ya ci gaba har ya kai ga nasara.

Jawabin Masu Sharhi

Masana harkokin siyasa sun ce jawabin Tinubu yana nuna irin ƙalubalen da 'yan siyasa ke fuskanta a kokarinsu na neman mulki, musamman a Najeriya inda tattalin arziki da siyasa ke da matukar wahala.

Kazalika, wasu sun bayyana cewa irin wannan ƙalubale na rashin kuɗi da matsalolin tattalin arziki da ya ambata su ne ke kara nuna irin halin da jama’a ke ciki a yau, musamman a lokacin da matsalar rashin takardun kuɗi ta dabaibaye Najeriya.

Tuni dai wannan jawabi ya fara janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke yabawa da irin juriya da ƙwazon da Shugaban ya nuna, yayin da wasu kuma ke ganin hakan wata hanya ce ta neman karin goyon bayan jama’a.