History : Tarihin Wani Mahaukaci Mai Wa'azi

Kissar wani mahaukaci mai suna Bahalu wanda ya rayu a zamanin shugaban Musulmi Harun Al-rasheed abu jafar ibn mansur khalifa a zamanin daular musulunci na abasi,

 

Wata rana mahaukaci baharu ya tafi bayan gari sai ya zaunna akan wani kabari, 

A dadai wannan lokaci Sarki Harun Al-rasheed ya fito tarreda masu himasa hidima tareda bashi tsaro, a wannan lokaci sai sarki Harun Al-rasheed  ya tadda bahalu akan wannan kabari. 


Sai Sarki Harun Al-rasheed yacema bahalu ya kai wannan mahaukaci wai kai sai yaushe zakayi hankali ne? A yayında wannnan mahaukaci bahalu yaji wannan kalami na sarki Harun Al-rasheed Sai yayi masa ya haukan wata itaciya cikin sauri da azama sannan ya daga muryarsa cikin murya mafi daukakawa sannan  yace: yakai harun sarki ! Wai yaushe ne kam zakai hankali? Lallai Wannan kalami inba dań ansan bahalu mahaukaci ne to tabbas a wannan lokaci da sai dai wani ba shiba ko kumą ya fuskanci hukunci mai tsananin gaske. Saboda a wannan zamanı babu wani mai yin motsi har idan sarki Harun na wucewa. koda jin haka sai sarki haroon ya zaburi dokinsa don kusantar itaciyar da bahalu ke bisa kanta, sai sarki harun ya daga kansa da siffa irinta ado da sarauta, ya kalli bahalu bisa kan wainna itaciya sannan yace masa; yanzu nine mahaukaci ko kai da na tadda kai bisa kan kabari?


Sai bahalu yace masa a’a sarki harun ai ni inada bankalı, sai sarki harun yace ma bahalu ai hakan baza ta taba ida kasancewa ba, nan take sai bahalu ya nuna yatsansa bisa gine ginen fadar  sarki Harun Al-rasheed wadanda gine gine ne na alfarma, gasu da kyau kuma sun gawurta. Sai bahalu yace ni na san cewa wadan can duk masu karewa ne, wannan kabarin shine tabbas shiyasa take raya shi kuma na dawo na tare wajenshi, kai ko sai ka ruguza naka kabarin kali ta gina benaye a duniya , bayan kasan wataran tabbas zaak koma cikinsa da zama ko kanaso ko baka so. Shiyasa baka son zuwa inda yake saboda ka riga da ka rusa shi (dikin tsawa da sauti mai girma) Mahaukaci bahalu ya cigaba da cewa: to yanzu dani da kai waye mahaukaxci a cikinmu ? 


Da jin haka sarki haruna yayi kuka matuka har hayyacinsa ya nemi fita, geminas duk ya jike cike da hawaye, sai sarki harun ya kalli bahalu a sama yace wallahi kayi gaskiya, sannan ya kara da cewa to dań Allah ka kara yimin wani wa’azin yakar bahalu,  sai bahalu yace ai littafin Allah Al-Qur’ani mai girma ya isheka wa’azi, harun yana jin haka sai ya fadi kasa cikin tsoron Allah sannan yacema bahalu, shin kana da wata bukata da kake so , ko mai cece ka fadi zan baya maka ita, a yayinda bahalu yaji haka sai yacema sarki almansoor e’ lallaikam inada wata bukata guda uku, sai sarki harun yace ka fadesu ko menene kuwa ni zam biyamaka bukatunka, da jin haka sai bahalu yace, na daya ka karamin yawan shekaruna a Duniya, na boyu yace ka kareni daga farmakin mala’ikan mutuwa, na uku ka tseratar dani daga wuta ka sani a aljanna. Da jin haka sai sarki harun yace wallahi bazan iyi ba koda ko a karan kaina ne, sai bahalu ce to invai hakane to vallai kaiko abin mulka ne ba abin mulki ba domin ko bąka da ikon komai a karan kanka sai abinda Allah ya yarda, saboda haka ni banida wata bukata a wojenka. Abin kiyayewa shine kada neman Duniya ya sana ka manta da Lahira , ka tuna duniya ba matabbata bane, ka rike Allah , ka bauta ta mishi ko ka sami babbar rabo ganar gobe kiyama, 



Allah ya kara mana imani ya tabbatar da dugadugan mu akan hanyar da ya yadda da ita muna musulmai masu imani, Allah ya kara mana son Manzon Allah Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.