History: Tarihin Shehu Ahmadu Tijjani - Shugaban Darikar Tijjaniyya

Shehu Ahmadu Tijjani (Abū al-ʻAbbās Ahmad ibn Muhammad at-Tijāniyy ko Ahmed Tijani) wanda ya shahara a arikar sufanci ta shehu adu tijjani mai suna shehu Ahmadu tijjani , ya kasance fitaccen malami kuma shugaban addini a kasashen yammacin afrika. Yayi fice wajen tarbiyyar ruhi da jajircewa akan koyarwar addinin muslunci da kuma bada gudumawa wajen yada darikar tijjaniyya a yankin. 

Shehu Ahmadu Tijjani



An haifi Shehu Tijjani a karni na 18, tasirin Shehu Tijjani ya zarce a rayuwarsa, yayin da karantarwarsa  ke ci gaba da yin tasiri ga al’ummar Musulmi a fadin Afirka, musamman a Najeriya, Senegal, da sauran kasashen Sahel. Tijjaniyya ita kanta darikar Sufaye ce wadda Sheikh Ahmad al-Tijjani ya kafa a karni na 18 a Arewacin Afrika. Darikar tana ba da fifiko kan sadaukar da kai ga Allah, karantarwa akai-akai da neman ilimi na ruhaniya. 


Shehu Ahmadu Tijjani ya taimaka wajen yada koyarwar wannan tsari, wanda ke karfafa zaman lafiya, hadin kai, da muhimmancin tafiya ta ruhi. 


Shehu Tijjani ba kawai jagora ne na ruhi ba, har ma ya kasance mai fafutukar ganin an gyara dabi'u da zamantakewar zamaninsa. Jagorancinsa ya kwadaitar da mutane da yawa da su yi rayuwa daidai da ka'idojin Musulunci na takawa, da sadaka, da kawo cigaban al'umma. 


A Najeriya tsarin Darikar Tijjaniyya ya karu sosai, musamman a yankunan Arewa, inda tayi karfi a harkar ilmin addinin Musulunci da rayuwar addini. Daga cikin manya manyan karantarwa Shehu Tijjani akwai “zikiri” (Ambaton Allah) da kuma cibiyarta ta zawiya (cibiyoyin ruhi), wadanda suke zama wuraren ibada da koyo ga mabiya. 


A yau, sunan Shehu Ahmadu Tijjani ya yi daidai da farfaɗowar Musulunci a yammacin Afirka, kuma ya kasance mutum ne mai matuƙar daraja a cikin Dariƙar Tijjaniyya, wanda malamai da muminai na gari suke girmama shi saboda tsoron Allah, jagoranci da sadaukar da kai ga tafarkin wayewar ruhi. 


Ga wasu daga cikin jerin sunayen sahabbansa:


Shehu Aliyul harazumi Al barrada

Shehu Mahmudu Tunusi

Shehu Alhaji Aliyul Tamasiyi

Shehu Muhammadun Nafarani

Shehu Kasimul Anna bi

Shehu Muhammadu binil Arabi Attazi

Shehu Muhammadul Mushuri

Shehu Muhammadul Gali

Shehu Ibrahimur Raiyahi

Shehu Ibrahimud dakkali

Shehu Abdul wahidul bannani Al misri

Shehu Daiyubul Sufyani

Shehu Ahmadu Sukairaju

Shehu Ahmadu Abdul lawi

Shehu Muhammadu binil Muhibbu Al zarhuni

Shehu Ahmadu Jas sus

Shehu Ahmadul Mugabbar

Shehu Hashim binil ma azuzu

Shehu musa binil Ma azuzu

Shehu Dahirul Akmari

Shehu Aliyul shatiwi

Shehu zu ununu

Shehu Muhammadu Nazifi

Shehu Ummarul Futi

Shehu Ibrahim inyasss inyasss inyasss