Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Soke Harajin VAT A Kan Iskar Gas Da Danginsa

A cikin kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi don rage dogaro da ababen hawa da ake amfani da man fetur a Najeriya tare da kokarinta na sauƙaƙa tsadar sufuri a kasar.



gwamantin ta Najeriya ta soke harajin VAT a kan nau’ikan mai na gas da illahirin dangin sa.

Wannan na daga cikin matakai da ƙoƙarin gwamnatin na karya farashin makamashi a ƙoƙarinta na bunƙasa amfani da ababen hawa masu amfani da gas ɗin CNG da LNG da man dizel da kuma wutar lantarki.