Tarihin Garin Agadez Da Ke Kasar Nijar

Garin Agadez gari ne mai cike da tarihi da al'adu, kuma garin yana tsakiyar hamadar sahara. An kafa birnin a kusan karni na 11, amma a wasu ruwayoyin sun nuna cewa yana iya yiwuwa an kafa shi tun kafin karnin na 11.

Wannan yana da tasiri matuka ba ma kasar Nijar ba kadai harma da kasashen da ke kewaye da ita, irin su Najeriya, Chad, Mali, Binin da Sauransu, saboda kasancewar ta mashiga ga kasashen ketare. Dalilin haka, garin ya sa Agadez ta zama muhimmiyar cibiyar kasuwanci da al'adu daban daban. A farkon shekarunta, Agadez ya bunƙasa a matsayin cibiyar kasuwanci. 'Yan kasuwa daga ko'ina cikin Afirka da sauran wurare suna zuwa saya da sayar da kayayyaki kamar zinariya, gishiri, masaku, har ma da bayi. 





A karni na 15, daular Songhai ta fadada tasirinta akan Agadez. Ƙarƙashin Songhai, birnin ya bunƙasa. Kasuwannin sun cika makil da kayayyaki daga kasashe daban daban. 


Abzinawa makiyaya, Hausawa 'yan kasuwa, da Fulani makiyaya, kowannensu ya kasance mai bada gudunmawa ta musamman wajen bunkasar birnin da hada-hada ta yau da kullum.


Al'ummar Abzinawa sun taka rawar gani a tarihin Agadez, sun yi amfani da iliminsu na hamada wajen bada kariya da tafiyar da hanyoyin shige da fuce na garin musamman ta hanyar kasuwanci bisa sahara. Agadez ta zama cibiyar al'adu da siyasa ga Abzinawa, wanda ke nuna al'adu da salon rayuwarsu.


Musulunci ya isa Agadez da wuri kuma ya shiga cikin al'adun birnin a karni na 16. Agadez ta zama cibiyar koyar da ilimin addinin musulunci, inda ta jawo malamai daga wurare masu nisa. Babban Masallacin Agadez, wanda aka gina a wannan lokaci, yana nuni da abubuwan tarihi na addini da na birnin. 


Doguwar hasuwaniyar masallacin mai cike da ban al’ajabi da ban mamaki  wadda aka yi gaba ɗaya da tubalin laka ta kasance abin ban sha’awa da duba ga ma’abota tarihin duniya da bibiyar al’adu.




A karshen karni na 19, daular mulkin mallaka ta Faransa ta fadada zuwa yammacin Afirka, kuma Agadez ta kasance karkashin mulkin Faransa. Faransa ta kafa sansanin soji tare da sarrafa hanyoyin kasuwancin garin. 


A karkashin mulkin mallaka, garin Agadez ya ga sauye-sauye da dama, ciki har da bunkasar ababen more rayuwa da sauyin yanayin mu’amala ta yau da kullum a tsakanin al’umma.


Nijar ta sami 'yencin kanta daga hannun Faransa a shekarar 1960, kuma Agadez ta kasance daga cikin bangarori na sabuwar jamhuriyar Nijar. 


A yau, garin Agadez ya kasance muhimmin birni wajen adana tarihi da al’adun duniya,  Ya adana da yawa daga ababe na tarihi kamar su tsoffin gine-gine masu yawan gaske wadanda har yanzu suna nan tsaye. 


Bugu da kari, birnin Agadez wuri ne na adana Tarihin Duniya na UNESCO, wato Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya.  


It UNESCO wata hukuma ce ta musamman ta Majalisar Dinkin Duniya (UN) wacce ke da nufin inganta zaman lafiya da tsaro a duniya ta hanyar hadin gwiwar kasa da kasa a fannin ilimi, fasaha, kimiyya da adana tarihi da al'adu.


A wannan zamani da muke ciki, bayan kasancewar garin Agadez cibiyar kasuwanci da mahadar jama’a, har ila yau ana hakar ma’adinan uranium da ake hada Nukiliya da su, wadanda ake hakowa a yankin da ke kewaye. 


An san birnin da kasuwar rakuma da sana'ar azurfa da kuma ta fata. A garin akwai cibiyar sufurin jiragen sama ta Agadez, an sanyawa filin jirgin saman suna “Mano Dayak” wato sunan wani shahararren shugaban Abzinawa.



A shekarun baya-bayan nan, garin Agadez ya zama wata babbar hanyar safarar bakin hauren Afirka ta Yamma da ke zuwa Libiya da Turai. Wannan ya kawo sabbin kalubale na zamantakewa da tattalin arziki a garin. 


A yau, Agadez birni ne da ke girmama tarihinsa mai tarin yawa yayin da yake tafiya da zamani.